Connect with us

Labarai

Hukumar KAROTA ta cafke barasa ta fiye da miliyan Hamsin

Hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Kano KAROTA, ta ce, ta kama wasu manyan motocin ɗaukar kaya guda biyu dauke da fiye da katan dubu biyu na barasku da kuɗinta ya haura Naira miliyan Hamsin.

Shugaban hukumar Baffa Babba Dan, agundi ne ya tabbatar da kamun yau Alhamis ta cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar Nabilusi Abubakar Ƙofar Na’isa, ya aiko wa www.kakakihausa.com

Sanarwar ta kuma ce, Baffa Babba ya bai wa jami’in da ya kama manyan motocin kyautar Naira miliyan ɗaya sakamakon ƙin karɓar cin hancin Naira dubu biyar domin ya saki motocin da ke ɗauke da barasar.

Sanarwar ta ruwaito cewa jami’in ya cafke motocin ne saboda gwamnatin jihar Kano ta haramta shigowa da barasa da kuma shan ta a jihar baki ɗaya don haka hukumar ta kuma ƴar uwarta, hukumar kare haƙƙin masu amfani da kayayyaki ta jihar Kano karkashin jagorancin shugaban KAROTA ba za su kyale duk wanda aka kama yana kai irin waɗannan kayan maye ba.

Shugaban na KAROTA, Ya yaba wa jami’in dan kishin ƙasa tare da jan hankalin sauran jami’ai’ da su yi koyi da shi kuma a koda yaushe su riƙa yin la’akari da tsaron rayuka da dukiyoyin jiha kafin yin komai.

A nasa ɓangaren Halilu Kawo Jalo, jami’in da ya kama haramtattun kayan, ya ce ya kama motocin ne ta hanyar amfani da masu ba da rahotonnin sirri da suka ba da bayanai game da kayan.

Ya ce, “Mun tare motocin ne a kan titin Obasanjo zuwa yankin Sabon Gari”.

Sun ba ni cin hanci amma na ƙi karɓa saboda na san illar barasa ga rayuka, kuma shan ta haramun ne, haka nan kuma ya saba wa koyarwar Musulunci karbar cin hanci, waɗannan ne suka sa na yi abin da ya dace,” inji shi.

Baffa ya kuma yi kira ga jama’a da su riƙa bai wa hukumarsa goyon baya domin tabbatar da tsaron jihar Kano.

 

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet