Addini
Hajj 2002: Alhazan Kano 260 Sun Dawo Daga Saudiyya
Alhazai 260 ne daga jihar Kano, wadanda suka halarci aikin Hajjin bana a kasar Saudiyya suka dawo kasa Najeriya a yammacin ranar Juma’ar nan.
Alhazan da suka hau jirgin AZMAN mai lamba ZQ2349 sun isa filin jirgin saman Malam Aminu Kano dake Kano da misalin karfe 02:41 na rana.
Babban Sakataren Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano, Alhaji Muhammed Abba-Danbatta ne ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Juma’a.
Ya ce alhazan sun kasance masu biyayya da bin doka a kasa mai tsarki.
Abba-Danbatta ya godewa gwamnatin jihar bisa tallafin da ta bayar a lokacin aikin.
Ya kuma yi godiya ga Allah da ya ba shi nasara tun daga farkon aikin Hajji har zuwa karshensa.
Sakataren zartarwa ya bayyana cewa ana sa ran dawowar kashi na biyu na maniyyata.
(NAN)
