Ilimi
Gwamnan Jihar Neja Ya Dakatar Da Shugaban Hukumar SUBEB
Gwamna Abubakar Bello na jihar Neja ya dakatar da shugaban hukumar kula da ilimin bai daya ta jihar Neja, Dakta Isah Adamu kan wasu matsalolin da hukumar ke fuskanta.
Dakatarwar na kunshe ne a cikin wata takarda mai dauke da sa hannun sakataren gwamnatin jihar Alhaji Ahmed Matane.
Matane ya kara da cewa, “wasu matsalolin rashin aikin yi ne suka sanya ta dakatar da aiki a hukumar .”
Gwamnati ta umurci Adamu da ya mika al’amuran hukumar ga mamba na uku a hukumar domin ba da damar sake duba ayyukanta domin samun ci gaba mai kyau.
(NAN)
