Connect with us

Labarai

Tinubu, Lawan, Dangote, Gwamnonin Sun Hallara A Maiduguri Domin Auren Diyar Shettima

Maiduguri ta yi cikar kwari a ranar Asabar din nan yayin da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu ya jagoranci wasu manyan mutane wajen halartar daurin auren diyar abokin takararsa Kashim Shettima.

Fadar shugaban kasa ta samu wakilcin shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Ibrahim Gambari da mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Babagana Monguno a wajen daurin auren.

NAN ta ruwaito cewa an biya sadaki gold coins 12 a matsayin sadaki a wajen bikin, wasu manyan baki da suka shaida sun hada da shugaban majalisar dattawa, Amed Lawan, Aliko Dangote, Dahiru Mangal, Ahmed Indimi, Gwamna Aminu Tambuwal na Sokoto da kuma takwaransa na Jigawa, Gwamna Abubakar Badaru.

KARANTA WANNAN; https://kakaki24.com/2022/07/30/likitoci-sun-baiwa-gwamnatin-tarayya-waadin-makwanni-2-kan-wasu-bukatu/

Gwamnoni kamr Mai-Mala Buni na Yobe, Kayode Fayemi na Ekiti, babbab sufeton yan sanda Usman Baba Alkali, da shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Adamu suma sun halarci taron.

An gudanar da daurin auren ne a fadar Shehun Borno inda Gwamna Zulum na Borno ya zama waliyyin Amarya Fatima, yayin da Ango Sadiq Ibrahim dan tsohon ministan babban birnin tarayya Abuja, Ibrahim Bunu ya wakilci tsohon Gwamna Bauchi, Ahmadu Muazu.

(NAN)

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet