Labarai
Jami’an hukumar NAFDAC sun janye yajin aikin da suke yi
Bayan shafe makonni biyar suna yajin aiki jami’an hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Najeriya NAFDAC, sun janye yajin aikin a yau Litinin.
Mataimakin shugaban ƙungiyar ma’aikatan Mista Idzi Isua, ne ya tabbatar da batun janye yajin aikin ga manema labarai a Litinin ɗin nan.
Ya ce, ƙungiyar ta janye yajin aikin ne sakamakon wata yarjejeniya da suka ƙulla da hukumar tasu.
Tun a ranar 21 ga watan Yunin da ya gabata ne ma’aikatan hukumar suka tsunduma yajin aikin a wani mataki na neman biyan su albashi da alawus-alawus.
