Connect with us

Labarai

Za mu gaggauta sahale kasafin kuɗin baɗi- Majalisar Dokokin Kano

Majalisar dokokin jihar jihar Kano, ta ce, za ta nanata gaggauta sahale daftarin kasafin kuɗin shekarar baɗi zuwa doka domin aiwatar da wasu muhimman ayyuka da shirye-shiryen da za su kawo ci gaba a jihar.

Hakan na ƙunshe ne cikin sanarwar da Sakataren yaɗa labarai na majalisar Uba Abdullahi ya fitar da yammacin yau Litinin.

Sanarwar ta ce, Shugaban majalisar Injiniya Hamisu Ibrahim Chidari, ne ya bayyana hakan yayin kammala taron bita na kwanaki biyu ga mambobin majalisar kan bunƙasa tattalin arziki da kasafin wanda aka gudanar a jihar Kaduna.

Chidari, wanda ya samu wakilcin mataimakin shugaban majalisar Alhaji Kabiru Hassan Dashi, ya bayyana cewa makasudin taron shi ne duba rahoton ayyukan kasafin rabin shekara ta 2022 da bunƙasa tattalin arziki da kasafin kudi, takardar dabarun kasafin kudi da kuma bayanin manufofin kasafin kudi, don shirin kasafin kudi na shekarun 2023 zuwa 2025 da kuma samar da kididdigar albarkatun kasa na kasafin jihar Kano na shekarar 2023.

Haka kuma, mataimakin shugaban majalisar ya yi kira ga ma’aikatar kasafin da sauran masu ruwa da tsaki da su ci gaba da yin amfani da cikakken amfani da dokar gudanar da hada-hadar kuɗi ta jihar Kano da majalisar ta amince da su.

A nasa jawabin sakataren gwamnatin jiha Alhaji Usman Alhaji ya ce taron bitar an tsara shi ne don bayyana yadda tsarin kasafin kudi ya dace a cikin matsakaicin lokacin kashe kudi wanda zai shafi manufofi da tsare-tsare da shirye-shiryen kasafin kudi domin bai wa mahalarta hanyar fahimtar yadda ake ware albarkatu ga dukkan bangarorin da suka dace bisa gaskiya kuma a kimiyance don bai wa dukkan ma’aikatu MDAs damar tsara wa da aiwatar da kasafin kudi tare da himma da kwarin gwiwa wajen isar da ayyuka da shirye-shirye don amfanin al’umma Kano.

Haka kuma sanarwar ta ce, A nasa jawabin shugaban ma’aikata na jihar Kano Alhaji Usman Bala MNI, wanda ya samu wakilcin babbar sakatare a ofishinsa Hajiya Fatima Fulani Sarki ya ce, taron ya zo a daidai lokacin da ya dace kuma ya nuna cewa gwamnati ta shirya kammala kasafin kuɗi na gaba yadda ya dace.

A jawabinsa na rufe taron, babban sakataren ma’aikatar kasafin kuɗi da tsare-tsare Alhaji Auwal Umar Sanda, ya bayyana jin daɗinsa kan abubuwan da aka tattauna yayin taron bitar na wuni biyu tare da tabbatar wa mahalarta taron cewa za a yi amfani da abubuwan da aka cimma ta hanyar da ta dace.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet