Connect with us

Labarai

Da Dumi-Duminsa: ‘Yan Ta’adda Sun Kara Sakin Mutum 5 Cikin Wadanda Harin Jirgin Abuja-Kaduna Ya Ritsa Da Su

Wasu mutane biyar da aka yi garkuwa da su a ranar 28 ga watan Maris a cikin wani jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna sun samu nasarar kubutar daga hannun ‘yan ta’adda.

Har yanzu hukumomin tsaro da gwamnatin tarayya ba su tabbatar da faruwar lamarin ba, sai dai wani mamba a cikin tawagar da suka sasanta, Tukur Mamu ya shaidawa gidan talabijin na Channels cewa an sako wadanda lamarin ya rutsa da su a ranar Talatar nan, 2 ga watan Agusta.

Ya bayyana sunayen mutane biyar da aka sako a matsayin sunayen wadanda aka yi garkuwa da su biyar da Farfesa Mustapha Umar Imam wanda ke aikin jinya a asibitin koyarwa na Jami’ar Usman Dan Fodio da ke Sokoto da Akibu Lawal da Abubakar Ahmed Rufai Mukthar Shu’aibu da Sidi Aminu Sharif.

Mamu wanda ya ce ya taka rawar gani wajen sako mutanen da jirgin kasan ya rutsa da su, ya bayyana cewa ya ja baya ne saboda barazanar da ake yi masa, da mutuncin sa da kuma rashin goyon bayan gwamnatin tarayya.

Ya zuwa yanzu, mutane 27 da abin ya shafa sun sake samun ‘yancinsu. Yayin da aka sako mutane biyar daga cikin wadanda aka sace, adadin wadanda har yanzu ake tsare da su ya kai 35.

Sai dai ba a bayyana ko an biya ‘yan ta’addan wani kudi domin su sako mutanen da aka sace ba.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet