Labarai
DA DUMI-DUMI: Gwamnatin Tarayya Ta Ci Tarar Trust TV Naira Miliyan 5
Gwamnatin tarayya a ranar Larabar nan ta ci tarar gidan Talabijin na Trust (Trust TV) naira miliyan biyar saboda watsa wani shirin fim mai suna ‘Nigeria’s Banditry: The Inside Story’’.
Solacebase ta ba da rahoton cewa tashar ta watsa shirin a ranar 5 ga Maris, na shekarar 2022.
Wata sanarwa da hukumar ta Trust TV ta fitar a ranar Larabar nan, ta ce hukumar kula da kafafen yada labarai ta kasa a cikin wata wasika mai dauke da kwanan watan Agusta 3, 2022, mai dauke da sa hannun babban darakta ta, Balarabe Shehu Illela, ta ce an ci tarar gidan talabijin na Trust saboda yada labaran da ta ce ya ci karo da sassan kundin tsarin yada labarai na kasa.
“Yayin da muke nazarin matakin da Hukumar ta dauka a halin yanzu da kuma yin la’akari da zabin, muna so mu bayyana babu shakka cewa a matsayinmu na gidan talabijin, mun yi imanin cewa muna yin abin da ya dace don amfanar da jama’a ne ta hanyar yin karin haske kan wannan kazamar matsalar ta ta’addanci da kuma yadda yake shafar miliyoyin mutane ‘yan kasarmu,” in ji sanarwar.
