Labarai
Wajibi Ne Mu Lashe Dukkan Zabukan 2023 — Inji Shugaban Jam’iyyar APC
Ya zama wajibi mu lashe zaben Shugaban Kasa, Gwamnoni, Da Dukkannin Zabukan 2023—Shugaban Jam’iyar APC
Shugaban jam’iyar APC na kasa Abdullahi Adamu ya bayyana cewa, ya zama wajibi jam’iyar ta lashe kafatanin zabukan da za’a gudanar a babban zaben shekarar 2023.
Adamu ya ce, wajibi ne APC ta samu gagarumin nasara a zaben shugaban kasa, Yan majalissu, da zabukan gwamnonin jihohi a 2023.
Yayin da yake zantawa da manema labarai a jiya Laraba a babban birnin tarayya Abuja Adamu ya jaddada cewa, Da yuwuwar Jam’iyar APC ba zata lamunci kashi 25 cikin dari kacal ba.
“Duk zabukan kasa, ‘yan majalisar wakilai, dattijai, gwamna, musammanma zaben shugaban kasa, ba za mu gamsu da kashi 25 na kuri’un da aka kada ba.
“Babu wata hanya bayan hakan, I dan za mu yi nasara, ya zama wajibi muyi kokarin lashe zaben a kowace jiha” inji Adamu.
.
Kazalika Shugaban jam’iyar APCn na kasa ya bukaci yayan jam’iyar da su tabbatar sun dinke barakar dake tsakanin su, domin samun nasarar Jam’iyar a babban zaben 2023.
