Connect with us

Labarai

Katsina: Ƴan sanda sun kuɓutar da mutane 6 daga maɓoyar ƴan garkuwa

Rundunar ƴan sandan jihar Katsina, ta ce ta kuɓutar da wasu mutane shida daga hannun masu garkuwa da mutane.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar SP Gambo Isah, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a ƙarshen makon nan.

 Ya ce, Ƴan sanda sun yi nasarar kuɓutar mutanen ne yayin wani sumame da suka kai sansanin ƴan bindigar a yankin ƙaramar hukumar Danja ta Jihar.

Haka kuma ya ce, ɓata garin sun yi sansani ne a ƙauyen Tandama inda jami’an suka kai musu farmaki a jiya Asabar bayan da suka samu bayanan sirri a kansu.

Rundunar ƴan sandan ta jihar Katsina ta bayyana sunayen mutanen da ta ceto da suka haɗar da: Alhaji Garba Dan Mallam mai shekara 52, Rabiu Idris mai 45, Abba Sama’ila mai 38, Yunusa Sani mai 54, Ishaq Yakub mai 40, Danjuma Sama’ila mai 45.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet