Labarai
Sokoto: Jami’an NDLEA sun cafke tsohon soja yana siyar wa ƴan bindiga ƙwayoyi
Hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi NDLEA shiyyar jihar Sokoto, ta ce, ta cafke wani tsohon soja mai shekara 90 bisa zarginsa da sayar wa ƴan bian fashin daji safarar ƙwayoyi.
Hakan na cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar a ƙarshen mako mai ɗauke da sa hannun mai magana da yawun hukumar na ƙasa Mista Femi Babafemi.
Sanarwar ta ce, jami’an hukumar sun cafke tsohon sojan Usman Adamu ne a ranar Laraba 3 ga wannan watan da muke ciki na Agusta a garin Mailalle na ƙaramar hukumar Sabon Birni.
Haka kuma ta cikin sanarwar, NDLEA, ta ce, ta same shi da Tabar wiwi mai nauyin Kilo giram 5.1.
