Labarai
An Shiga Zulumi A Abuja Yayin Da ‘Yan Sanda Suka Yi Arangama Da Yan Daba
An Shiga Zullumi A Abuja Yayin Da ‘Yan sanda Suka Yi Arangama Yan daba
A ranar Litinin da ta gabata ne aka samu barkewar sa’insa a yankin Jikwoyi na hanyar Nyanya zuwa Karshi a Abuja, yayin da jami’an tsaro suka yi arangama da wasu ‘yan daba da aka ce sun kashe dan sanda cikin dare a yankin.
Shedun gani da ido sun tabbatar da cewa harin ya haifar da tarzoma daga a yayin da ma’aikata da matafiya ke kan hanyarsu ta zuwa tsakiyar birnin.
An ce rikicin ya shafi jami’an ‘yan sanda da ‘yan tada zaune tsaye karkashin wani mutum da aka fi sani da “Mai bolas.” wadanda suka kona akalla mota daya.
An ce jami’an tsaron sun fatattake su har maboyarsu da ke kewayen yankin, inda daga baya aka tarwatsa su.
A yayin da rikicin ya yi kamari, an hana zirga-zirgar ababen hawa a sassan biyu na hanyar Nyanya zuwa Karshi, yayin da direbobin ke jujjuyawa don gujewa fadawa cikin tashin hankali.
Rundunar hadin gwiwa ta jami’an tsaro ta ce ta yi nasarar fatattakar ‘yan ta’addan tare da kame da dama daga cikinsu kafin a maido da doka oda a yankin.
