Labarai
‘Yan Bindiga Sun Saki Wasu Fasinjojin Jirgin Kasa Bakwai Da Aka Yi garkuwa da su
Karin wasu fasinjoji bakwai da aka yi garkuwa da su a harin jirgin kasa na ranar 28 ga watan Maris a jihar Kaduna sun samu ‘yanci.
An sako mutanen da aka sace a safiyar ranar Larabar nan bayan sun shafe kwanaki 135 a hannun ‘yan ta’addan.
Sai dai ba a bayyana ko an biya kudin fansa ga ‘yan ta’addar domin a sako su ba.
Ko da yake hukumar ‘yan sanda ba ta tabbatar da faruwar lamarin ba, wani mamba a tawagar da suka shiga tattaunawar, Tukur Mamu ya shaidawa gidan talabijin na Channels cewa shida daga cikin wadanda aka sako ‘yan gida daya ne, wadanda suka hada da ma’aurata da ‘ya’yansu hudu.
Mahaifin ‘ya’yan hudu, Abubakar, dan tsohon shugaban mulkin soja ne na jihohin Kano da Benue, ga Mamu, Manjo Janar Chris Garba, kuma ma’aikaci ne a Majalisar Dokoki ta Kasa.
‘Yan ta’addan sun kuma sako wata mata ‘yar shekara 60, Hajiya Aisha Hassan wadda aka ce an kubutar da ita ne sakamakon kalubalen rashin lafiya da ke barazana ga rayuwata a baya-bayan nan.
Sunayen ‘yan uwa 6 da aka saki sune Abubakar Idris Garba wanda shi ne mahaifin ‘ya’yan hudu, matarsa Maryama Abubakar Bobbo da babban dansu, Ibrahim Abubakar Garba mai shekaru 10.
Sauran sun hada da Fatima Abubakar Garba ‘yar shekara 7 da Imran Abubakar Garba mai shekaru 5 da karama Zainab Abubakar Garba mai shekara daya da rabi kacal.
Ya zuwa yanzu, mutane 42 da abin ya shafa sun sake samun ‘yancinsu. Adadin wadanda har yanzu ake tsare da a hannun masu garkuwar ya kai 35.
A ranar 28 ga watan Maris ne wasu ‘yan bindiga suka tarwatsa titin jirgin, inda suka kashe wasu tare da yin awon gaba da fasinjoji da dama, lamarin da ya bukaci a nuna matukar damuwa game da tsaron lafiyar jiragen kasar.
Sakin ranar Larabar nan na zuwa ne kwanaki kadan bayan wasu ‘yan ta’addan sun sako wasu mutane biyar da suka yi garkuwa a jirgin zuwa Kaduna.
Wadanda aka ceto sun hada da Farfesa Mustapha Umar Imam, wanda likita ne a asibitin koyarwa na Jami’ar Usman Dan Fodio, da ke Sokoto, da Akibu Lawal, sai Abubakar Ahmed Rufai Mukthar Shu’aibu da Sidi Aminu Sharif.
Sun sami ‘yancinsu a ranar 2 ga Agusta, sun kuma koma ga danginsu.
Gidan Talabijin na Channels ya tattaro cewa ‘yan ta’addan sun sako su ne a wani wuri da ke cikin dajin da ke kan hanyar Kaduna zuwa Abuja. Daga nan ‘yan uwansu ne suka karbe su.
Dangane da halin da ake ciki, hukumar kula da zirga-zirgar jiragen kasa ta Najeriya ta dakatar da ayyuka na wani dan lokaci, inda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umurci hukumomin tsaro da su ceto wadanda lamarin ya shafa.
