Labarai
Hajjin Bana: Mahukuntan Saudiyya sun sanar da ranar kammala kwashe alhazai
Mahukuntan ƙasa mai tsarki, sun sanya ranar Asabar 13 ga wannan wata da muke ciki na Agusta a matsayin ranar da za’a kammala kwashe alhazan bana baki ɗaya.
Hukumar kula da aikin Hajji da Umara ta ƙasar, ta cikin sanarwar da ta fitar ta umarci kamfanonin jiragen da sukayi jigilar alhazan da su tabbatar sun kammala kwashe alhazan a wannan wa’adi.
