Labarai
Gwamnatin Jihar Zamfara Za Ta Kashe Naira Miliyan 700 Domin Gyaran Gadoji Da Titina
Gwamnatin Jihar Zamfara Za Ta Kashe Naira Miliyan 700 Domin Gina Gadoji Da Titina
Gwamnatin Zamfara a ranar Juma’ar nan ta ce ta ware Naira miliyan 700 domin sake gina gadoji guda biyar da kuma tituna a fadin kananan hukumomi hudu.
Kwamishinan ci gaban al’umma, Alhaji Abdullahi Gurbin-Bore ne ya bayyana haka a wajen kaddamar da ayyukan da aka gudanar a Burgediya ta 1, Kantonment na Sojojin Najeriya da ke Gusau a Jihar Zamfara ranar Juma’a.
Kwamishinan ya lissafo gadojin da suka hada da kauyen Maigungumi da kauyen Tofa dake kusa da Dansadau, karamar hukumar Maru; gadar kauyen Badoki, gadar Gurusu da Nasarawa Bukulu a karamar hukumar Bukuyum, da kuma gadar Ruwan Gora da ke yankin Talata Mafara.
Aikin ya kuma hada da hanyar shiga makarantar Staff School of 1 Brigade mai tsawon mita 500, da ke Gusau.
Ya ce amincewa da aikin ya biyo bayan korafe-korafen al’ummomin da abin ya shafa.
Gurbin-Bore ya ce wasu gadojin da abin ya shafa sun lalace tun shekaru hudu da suka gabata.
Kwamishinan ya ba da tabbacin cewa aikin, wanda ake gudanar da shi ta hanyar aiki kai tsaye, za a kammala shi cikin kankanin lokaci domin samun shige da fice a al’ummomin da abin ya shafa.
(NAN)
