Featured
An tuhumi mutumin da ya yi yunƙurin kashe Salman Rushdie
Abdu Ado Ƙofar Na’isa
Ana cigaba da tsare Hadi Matar mutumin da ya yi yunƙurin kashe marubuci Salman Rushdie wanda ya yi batanci ga Manzon tsira S.A.W. ta hanyar daba masa wuƙa a wuya a birnin New York na ƙasar Amirka.
Jami’an tsaro sun gudanar da shi ne a gaban kotu a jiya Juma’a kan zargin yunƙurin kisa na ci gaba da tsare shi ba tare da beli ba.
Hadi Matar mai shekaru 24 wanda ya daba wa marubucin wuka a yayin da yake jawabi a kan mumbari, bai kai ga cewa komai ba a game da wannan lamarin. Sai dai jami’an tsaro sun ce suna ci gaba da yi masa tambayoyi domin sanin manufarsa na kai wannan hari.
Marubucin da ke zama dan asalin kasar Indiya ya shafe shekaru yana buya bayan da kasar Iran ta halasta jininsa bisa wani littafi da ya rubuta mai sunan “Satanic Verses”.
Ya zuwa yanzu Mista Rushdie na kwance a asibiti cikin wani mawuyacin hali da masu aiko da rahotanni suka ce baya ko iya magana kuma akwai yiwuwar ya rasa idonsa a sabili da wannan harin.
