Connect with us

Featured

AZMAN ya bayyana nasarar da ya samu yayin aikin hajjin bana

Kamfanin Jirgin sama na AZMAN AIRLINE ya bayyana aikin hajjin bana na shekarar 2022 a matsayin wata nasara da cigaba da suka samu.

Bisa ga jigilar maniyyata 7,300 da kuma rundunar sojojin da hukumar HAHCON ta ware wa kamfanin daga jihohi 16 na tarayyar Najeriya.

Co-odinetan aikin Hajji na kamfanin jiragen saman Azman, Injiniya Nuraddeen Aliyu ne ya bayyana haka a wata tattaunawa da manema labarai a ranar Lahadi a Kano.

A cewarsa, duk da cewa sun bayyana a ƙurarren lokaci, amma sun sami damar jigilar dukkan fasinjojin nasu.

Ya kuma ce sun dauki Alhazan jirgin yawo kimanin 2500 kuma sun yi hulda dasu cikin aminci, kuma sun kai su sun kuma dawo dasu akan lokacin da suka dauka.

Alhazan sun fito ne daga jihohin Sokoto da kebbi da Gombe da Bauchi da Maiduguri da Kaduna da Yobe, da kuma jihar Kano.

“Mun samu matsala da jihar Kano kuma a lokacin da suka ki karbarmu a matsayin nasu, hakan ya sa muka fara da wasu jihohin.

A karshen aikin ne suka karɓe mu kuma muka dauki kashi na farko alhazai 400, amma kashi na biyu ya samu jinkiri saboda rashin shiri.

Bisa la’akari da halin da ake ciki a wancan lokacin da kuma wa’adin da hukumomin Saudiyya suka bayar, sai muka rubuta wata takarda zuwa ga NAHCON ta sake samar da wani lokacin da kamfanin jirgin da zai ceto Alhazan jihar Kano.

Duk da cewa sun amince da bukatarmu, amma hakan bai samu ba, don haka matsalar ba daga wurinmu ba ce,” inji shi.

Sai dai duk da wasu matsaloli da aka samu a lokacin da aka fara aikin, fuska ta biyu ta samu gagarumar nasara bayan dukkan fasinjoji tare da karin jami’an NAHCON kimanin 150 sun yi nasarar komawa gida a jirgin.

Injiniya Aliyu ya kara da cewa, babban kalubalen da suka fuskanta a lokacin aikin Hajjin bana shi ne ci gaba da fuskantar karancin man jiragen sama a Najeriya, wanda ya tilasta musu komawa Lagos don neman mai kafin su koma Jiddah, lamarin da ya haifar da tsaikon da bai kamata ba.

Nuraddeen ya ci gaba da alakanta jinkirin shirye-shiryen da hukumar Alhazai ta Najeriya ta yi da kuma jinkirin da gwamnatin Saudiyya ta bayar a matsayin manyan dalilan da ke kawo tsaikon.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet