Labarai
Hukumar KAROTA ta cafke wasu matasa da ke yin sojan gona da kakinta
Hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Kano KAROTA, ta cafke wasu matasa uku suna sojan-gona da hukumar.
KAROTA ta cafke matasan ne dai-dai lokacin da suke kan aiki akan titin Independence misalin ƙarfe 2:30 na dare.
Hukumar ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da jami’inta na yaɗa labarai Nabilusi Abubakar Ƙofar Na’isa, ya raba wa manema labarai ciki har da Shafin Kakakihausa.com
Ta cikin sanarwar hukumar ta ce, matasan sun haɗa da Lawan Ahmad Habibu da Abubakar Sale Muhd da kuma Shamsu Ibrahim dukkansu mazauna garin Kano.
Bayan da Hukumar ta cafke su sai suka shaida mata cewa suna gudanar da aikinsu ne tare da Lawan Ahmad Habibu tsohon jami’in Hukumar wanda tuni Hukumar ta jima da korarsa daga aiki saboda wannan mummunar ta’ada.
Haka, kuma Hukumar na ci gaba da kira ga jama’a musamman direbobi da su guji bayar da na-goro ga jami’an KAROTA wanda hakan ke zubda mutuncin aikinsu.
Tuni dai hukumar ta miƙa su hannun Rundunar ‘Yansanda ta jihar Kano domin ta faɗaɗa bincike tare da ɗaukar matakin gurfanar da su a gaban Shari’a
Shugaban hukumar ta KAROTA Baffa Babba Ɗan’agundi ya shawarci al’umma da su cigaba da kai rahoton duk wani jami’in da suka ga yana karɓar na-goro domin ya fuskanci tuhuma.
