Connect with us

Labarai

Mutum Hudu Sun Kara Samun ‘Yanci Cikin Wadanda Harin Jirgin Abuja-Kaduna Ya Shafa

Wasu ‘yan ta’adda da suka kai hari kan wani jirgin kasa AK9 a jihar Kaduna a ranar 28 ga watan Maris, sun sake sake wasu mutane hudu da aka yi garkuwa da su da ke hannunsu.

Daga cikin wadanda aka saki sun hada da wata mata mai shekaru 85, Hajiya Halimatu Atta da diyarta mai shekaru 53, da kuma wani mai suna Adama Aliyu.

Wani mamba a tawagar da suka sasanta, Tukur Mamu ya shaidawa gidan talabijin na Channels cewa an sako mutanen ne a ranar Juma’ar nan bayan shafe sama da watanni hudu a hannunsu.

A halin da ake ciki, Mamu ya ja kunnen Gwamnatin Tarayya da Kungiyar Kiristoci ta Najeriya game da shirin da ‘yan ta’adda suka yi na aurar da ‘yar karamar yarinya, Azurfa Lois John mai shekaru 21 a duniya, kamar yadda suka yi a kan Leah Sharibu a jihar Yobe a shekarun baya.

A cewar Mamu, daya daga cikin manyan kwamandojin ‘yan ta’addan an ce yana soyayya da Ms John.

Sai dai ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da sauran masu ruwa da tsaki da su kara zage damtse wajen ganin an sako mutane 23 da har yanzu suke tare da ‘yan ta’addan wadanda yanayin lafiyarsu, a cewarsa, na da matukarp ban tausayi da bukatar kulawar gaggawa.

Mamu ya kuma yi kira ga kungiyar CAN da kada ta sanya siyasa a lamarin, ko kuma ta mayar da shi zuwa ga sanarwar manema labarai kawai, amma da ta hada kai da hukumomin da abin ya shafa don shawo kan masu garkuwa da mutanen kan lamarin Ms John tun kafin lokaci ya kure.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet