Connect with us

Featured

Karim Benzema ya lashe kyautar gwarzon dan wasan Turai na bana

Daga Abdu Ado Ƙofar Na’isa

Dan wasan gaban Faransa Karim Benzema ya lashe kyautar gwarzon UEFA na bana, bikin da aka gudanar da shi a Istanbul na kasar Tukiyya a jiya Alhamis

Baya ga Benzema, bangaren mata yar Spain Alexia Putellas, ce ta lashe kyautar na wannan karo.

Karim Benzema mai shekaru 34, da ke taka leda a Real Madrid ya samun wannan nasara a kan yan wasa da suka hada Thibaut Courtois da ke kungiyar ta Real Madrid da kuma dan kasar Belgium daga Manchester City Kevin de Bruyne.

Karim Benzema ya zura kwallaye 44 a wasanni 46 da ya yi da Real, banda hakan, dan wasan ya yi nasara a gasar zakarun Turai tare da kungiyar Faransa.

Yanzu kam Benzema ya kama hanyar lashe kytautar Ballon D’or na farko kamar dai yadda hasashe ya nuna a yayin bikin da za a yi ranar 17 ga Oktoba a birnin Paris na kasar Faransa.

Tsohon dan wasan kungiyar Lyon, Karim Benzema ya zama dan wasan Faransa na biyu da ya samu wannan kyautar daga hukumar kwallon kafar Turai, bayan Franck Ribery da ya lashe wannan kyauta a 2013.

Kafin shi, yan wasan Real Madrid biyu ne suka taba lashe wannan kyauta: Wato Cristiano Ronaldo a shekarun 2014, 2016, 2017 da Luka Modric a shekarar 2018.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobetholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet