Labarai
An Kori Wasu Sojoji Biyu Daga Aiki Bisa Zargin Kisan Wani Malamin Addini
Rundunar sojin Najeriya ta kori wasu sojoji biyu bisa kisan wani malamin addinin Islama, Sheikh Goni Aisami a Gashua, da ke jihar Yobe.
Sojojin da aka kora sun hada da Lance Kofur John Gabriel da Lance Kofur Adamu Gideon.
Mukaddashin kwamandan da ke kula da bataliya ta 241 Reece da ke Nguru a jihar Yobe, Laftanar Kanar Ibrahim Osabo, ya shaida wa manema labarai cewa kwamitin binciken hadin gwiwa da aka kafa tare da hadin gwiwar ‘yan sanda ta same su da laifi.
Ya ce an sallami sojojin biyu ne bisa tuhume-tuhume biyu na rashin yin ayyuka da kuma nuna kyama ga horon aikin.
Laftanar Kanar Osabo ya kara da cewa za a mika sojojin da aka kora a hannun ‘yan sanda a Damaturu domin gurfanar da su a gaban kotu.
Kisan Gashua
Gidan Talabijin na Channels ya bada labarin kashe Sheikh Goni Aisami-Gashua a farkon watan nan.
An ce malamin yana tafiya ne daga Gashua zuwa Kano, yayin da maharan suka bi shi a cikin motar safa.
Wasu mazauna Gashua sun shaida wa gidan talabijin na Channels cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 10 na safe a Jajimaji mai tazarar kasa da kilomita 30 daga Gashua, mahaifar shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Dungus Abdulkarim, a wata zantawa da wakilinmu ta wayar tarho, ya ce an kama wadanda ake zargin dauke da bindigogi kirar AK-47 kuma suna hannun ‘yan sanda.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi Allah-wadai da kisan.
