Labarai
Allah ya yi wa Sarkin Funakaye Alhaji Mu’azu Muhammad Kwairanga III rasuwa
Allah ya yi wa Sarkin Funakaye da ke jihar Gombe Alhaji Mu’azu Muhammad Kwairanga III rasuwa.
Rahotonni sun bayyana cewa Sarkin ya rasu ne a ƙarshen makonnan, kuma ana sa ran za a yi jana’izarsa da almurunnan a fadarsa da ke garin Bajoga.
BBC ta ruwaito cewa yau kimanin watanni goma sha biyar kenan da aka naɗa shi a matsayin sarki bayan rasuwar babban yayansa Alhaji Abubakar Kwairanga a ranar 20 ga watan Mayun 2021.
Haka kuma ta ruwaito cewa, Ko a jiya Asabar sarkin ya halarci wani taro a birnin Gombe tare da ministan sadarwa, Farfesa Isa Ali Pantami.
Babu dai wasu bayanai da aka fitar kan abin da ya yi ajalinsa.
