Labarai
Kebbi: Ƴan sanda sun cafke wata mata bisa zarginta da kashe alƙali
Rundunar ƴan sandan Jihar Kebbi, ta cafke wata mata mai shekaru 30 bisa zargin ta da laifin kashe tsohon mijin ta.
BBC ta ruwaito cewa, jami’in hulɗa da jama’a na rundunar SP Nafiu Abubakar, ne ya tabbatar mata da cafke matar.
Ya ce, matar da aka kama ɗin tsohuwa matar wanda ake zargin ta hallaka ne wanda alƙalin kotun majistare ne mai suna Attahiru Ibrahim Zagga.
Ya ƙara da cewa, da misalin ƙarfe 9:00 na daren ranar Alhamis ne maƙobta suka kai wa ƴan sanda rahoton cewa sun ji hayaniya a gidan alƙalin da ke unguwar Alieru a birnin Kebbi.
Ya kuma ce “Da isar jami’anmu ne suka tarar da Attahiru kwance cikin jini, inda suka garzaya da shi asibiti kuma a can ne likitoci suka tabbatar da mutuwar sa”.
“Bayan shigar jami’anmu gidan suka tarar da tsohuwar matarsa mai suna Farida Abubakar kuma aka kama ta da zargin hannunta a aikata kisan,”
Haka kuma ta ruwaito cewa kafin rasuwar Attahiru Ibrahim alƙalin kotun majistare ne a garin Jega.
