Featured
Ambaliyar Ruwa: Atiku ya tallafa wa ƴan kasuwar Kwari da Naira miliyan 50
Ɗan takardar shugaban ƙasa a zaɓen baɗi na jam’iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar, ya bai wa ƴan kasuwar Kantin Kwari tallafin naira miliyan 50.
Tallafin nasa dai na a matsayin gudunmawa bisa iftila’in ambaliyar ruwan sama da kasuwar ta fuskanta a kwanakinnan.
Atiku Abubakar, ya sanar da bada tallafin ne yau Litinin a gidan Sanatan Kano ta tsakiya Malam Ibrahim Shekarau da ke unguwar Munduɓawa a Kano.
Kasuwar ta Kantin Kwari na daga cikin wuraren da suka gamu da iftila’in ambaliyar ruwan wadda wasu sassan jihar Kano da dama suka fuskanta.
