Labarai
Kano: Majalisar dokoki ta sake tantancewa tare da amincewa da naɗin sabon kwamishina
Majalisar dokokin jihar Kano, ta tantance tare da amincewa da naɗin Kabiru Muhammad Tarauni, a matsayin kwamishina.
Majalisar ta amince da shi ne bayan da ta tantance shi a zamanta na yau Litinin bayan da gwamna Ganduje ya aike mata buƙatar hakan ta cikin wata wasiƙa.
Kabiru Muhammad Tarauni, dai shi ne mutum na goma sha ɗaya da majalisar ta tantance tare da amincewa da su a matsayin kwamishinoni.
Premier Radio ta ruwaito cewa Kabiru Muhammad Tarauni, ya taɓa zama ɗan majalisar dokokin Kano karo biyu daga shekarar 2003 zuwa 2011.
