Labarai
Gwamnatin shugaba Buhari za ta ciyo bashi Naira Tiriliyan 11
Ministar kuɗi, kasafi da tsare-tsare ta Najeriya Hajiya Zainab Ahmed ta ce, gwamnatin tarayya za ta ciyo bashin naira Tiriliyan goma sha ɗaya tare da sayar da wasu manyan kadarori domin samun kuɗin da za a cike giɓin kasafin kuɗin baɗi.
Ministar ta bayyana hakan ne a Litinin ɗin makon nan lokacin da ta je gaban kwamitin kuɗi na majalisar wakilai domin gabatar da tsarin kashe kuɗi na matsakaicin wa’adi na shekarar 2023 zuwa 2025.
BBC ta ruwaito cewa, Ministar ta ce, ana sa ran gibin kasafin kuɗin zai zarta naira tiriliyan goma sha biyu.
Yayin da take bayanin hanyoyin biyu da za a cike gibin ga kwamitin, Ministar ta ce hanya ta farko ta hadar da ci gaba da biyan tallafin man fetur a ilahirin shekarar 2023
Ta ce hanya ta farko an yi hasashen cewa gibin zai kai naira Tiriliyan 12.41 a 2023, idan haka bi wannan hanya gwamnati za ta kashe tiriliyan shida kan tallafin man fetur
Haka kuma ta ƙara da cewa, Hanya ta biyu kuma ta kunshi ci gaba da biyan tallafi zuwa watan Yunin 2023, a wannan kuma gibin zai kai naira Tiriliyan 11.30, inda ake hasashen tallafin da za a biya zai kai naira tiriyan uku da biliyan uku.
