Featured
Chelsea ta kammala ciniki da Barcelona kan Aubameyang
Daga Abdu Ado Ƙofar Na’isa
Kungiyar kwallan kafar Chelsea ta kammala cinikin daukar ‘dan wasan gaba na kungiyar Barcelona, Pierre-Emerick Aubameyang akan kudi Fam miliyan 12, tare da wani dan wasan baya Marcus Alonso.
Aubameyang mai shekaru 33 shine dan wasa na 7 da Chelsea ta saya a wannan kaka domin karfafa kungiyar wadda ke fuskantar matsaloli a gasar Firimiya ta bana.
‘Dan wasan wanda dan assalin kasar Gabon ne, a shekarar da ta gabata ya koma Barcelona daga Arsenal sakamakon karewar kwangilar sa da kuma matsalar da ya samu da mai horar da kungiyar Mikel Arteta.
Sauran ‘Yan wasan da Chelsea ta saya bana sun hada da Wesley Fofana da Raheem Sterling da Kalidou Koulibaly da Carney Chukwuemeka da Marc Cucerella da kuma Cesare Casadei.
Yanzu haka Chelsea na matsayi na 9 a teburin Firimiya da maki 7 daga wasanni 5 da ta buga, abinda ya kaiga tsokaci dangane da makomar mai horar da Yan wasa Tomas Tuchel.
