Labarai
Dakarun Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda Uku, Sun Kwato Makamai A Kaduna
Dakarun runduna ta daya sun kashe ‘yan bindiga uku a yankin Sabon Birni, Dogondawa-Kuyelo da Farin Ruwa a jihar Kaduna.
Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadin nan, inda ya ce an kashe ‘yan bindigar ne a wani sumame da suka kai ranar Asabar.
Duk da cewa Nwachukwu ya kasa tabbatar da jimillar ‘yan bindigar da sojojin suka shiga ciki, amma ya bayyana cewa an samu ci gaba a kokarin da sojojin ke yi na kawar da ‘yan fashi da ta’addanci a yankin arewa maso yamma.
Kayayyakin da aka kwato daga hannun masu laifin sun hada da bindigogi kirar AK 47 guda biyu, mujallu guda tara, rediyon sadarwa na Baofeng guda bakwai, wayar salula ta Tecno daya, harsashi na musamman guda 120 mai girman milimita 7.62, injin samar da wutar lantarki daya da babur.
Sanarwar ta kara da cewa, “Dakaru masu karfi da kuzari, yayin da suke sintiri a yaki, sun yi karo da wasu ‘yan bindiga da ba a tabbatar da adadinsu ba.”
“Dakarun da suka yi harbin sun kashe 3 daga cikin ‘yan ta’addan tare da kwato bindigogi kirar AK 47 guda biyu, mujallu 9, rediyon sadarwa na Baofeng guda bakwai, wayar salula ta Tecno daya, harsashi na musamman guda 120 mai girman mili mita 7.62, injin samar da wutar lantarki daya da kuma babur.
Gidan talabijin na channels ya rawaito cewa, Da yake mayar da martani, babban hafsan sojin kasa (COAS) Laftanar Janar Faruk Yahaya ya yabawa sojojin bisa jajircewar da suke yi, ya kuma bukace su da kada su sassauta har sai an kawar da ‘yan fashi a yankin.
Hakazalika, babban kwamandan runduna ta daya, Manjo Janar Taoreed Lagbaja ya bukaci dukkan ‘yan kasa masu bin doka da oda da su ci gaba da tallafa wa sojoji da sauran hukumomin tsaro da sahihan bayanai masu inganci.
Bayanin, Lagbaja ya bayyana, zai taimaka wa sojojin a ayyukan da suke yi na yaki da masu aikata laifuka.
Jaridar Alkiblah Jihar Kaduna dai na daya daga cikin jihohin da suka fi fama da ‘yan ta’adda, inda suka kai hare-hare da dama tare da kashe mutane da yin garkuwa da wasu da dama.
