Labarai
Jigawa: Mata 4 da jariri ya ɗaya sun mutu a hatsarin Kwale-kwale
Rundunar ƴan sandan jihar Jigawa, ta tabbatar da mutuwar wasu mata huɗu da kuma jaririya ƴar wata bakwai sakamakon hatsarin kwale-kwale da ya ritsa da su a ƙaramar hukumar Guri.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar DSP Lawan Shisu Adamu, ne ya bayyana hakan a Dutse babban birnin jihar.
Ya ce, hatsarin ya faru ne da yammacin jiya Talata bayan da waɗanda lamarin ya ritsa da su suka hau kwale-kwalen daga ƙaramar hukumar Nguru ta jihar Yobe zuwa ƙauyen Adiyani na ƙaramar hukumar Guri ta jihar Jigawa.
Haka kuma ya ƙara da cewa, mai tuƙin kwale-kwalen ya tsira da ransa inda kuma dukkan mutanen da ya ɗakko ɗin suka nutse.
BBC ta ruwaito cewa, DSP Lawan ya kuma ce an kai gawarwakin matan cibiyar lafiya ta Adiyani inda babban likitan asibitin ya tabbatar da rasuwarsu.
