Jaridar Solacebase ta ruwaito cewa Sarkin Barjin Ibbi kuma shugaban masu aiki da jiragen ruwa a yankin Abdulrazak Abubakar Maito ne ya tabbatar da faruwar lamarin yana mai cewa zuwa yanzu an lalubo gawarwaki biyu.
Haka kuma ya ƙara da cewa ana aikin ci gaba da neman sauran biyun a cikin kogin.
Shi ma a nasa ɓangaren, Shugaban ƙaramar hukumar Ibbin Dakta Bala Baƙo da shi ma ya tabbatar da faruwar hatsarin ya kuma buƙaci gwamnatin Jihar da ta tarayya da su kawo musu agajin gaggawa domin rayuwar mazauna yankin na cikin hatsari.
