Connect with us

Labarai

Yajin Aikin ASUU: Zanga-zangar Dalibai Ta Janyo Babban Cinkoson Ababen Hawa

Dubban matafiya ne suka makale a kan babbar hanyar Ibadan zuwa Ife a ranar Alhamis din nan bayan da kungiyar dalibai ta kasa (NANS) ta yi toshe kan hanyar Gbongan Bypass.

Daliban dai na zanga-zangar nuna adawa da yajin aikin watanni tara da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ta shiga.

Da yake magana da gidan talabijin na Channels, kakakin NANS, Giwa Yisa Temitope, ya ce daliban Najeriya sun gaji da zama a gida. Ya kara da cewa gwamnatin tarayya ta gaza.

A ranar Larabar nan ma daliban sun tare babbar hanyar Legas zuwa Ibadan domin nuna rashin amincewarsu da takaddamar da ta kunno kai tsakanin kungiyar ASUU da gwamnatin tarayya. Sun toshe sassan shiga da fita na babbar hanyar.

Yayin da suke jawabi ga manema labarai a yayin zanga-zangar, mambobin kungiyar sun ce zanga-zangar ta zama wajibi domin su maida martani ga bukatarsu ta neman a gaggauta warware takaddamar da ke tsakanin kungiyar ASUU da gwamnatin tarayya.

Zanga-zangar ta kawo dakatar da zirga-zirgar ababen hawa a kan babbar hanyar da ya janyo cunkoso, inda fasinjojin suka makale. Wasu dai an tilasta musu bin hanyoyin da ba su dace ba don gujewa masu zanga-zangar, yayin da wasu kuma suka nuna adawa da cunkoson ababen hawa domin shawo kan abun da zanga-zangar ta haifar.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetRadissonbetsweet bonanzasweet bonanzapadişahbettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetholiganbetholiganbetholiganbetmarsbahismarsbahisjojobetjojobetjojobetcasibomcasibomcasibomholiganbetholiganbetjojobetjojobet girişjojobet güncel girişjojobet güncel girişgrandpashabetholiganbetholiganbetgrandpashabetcasinolevantimajbetsekabetjojobetjojobet girişgrandpashabetgrandpashabetTürkiyenin Casino Sitelerivdcasinograndpashabetgrandpashabet girişGrandpashabetsahabetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetmatbetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobetjojobet