Connect with us

Labarai

NNPP ta zargi jam’iyyar APC da shirin siyan katinan zaɓen mutane

Sabuwar Jam’iyyar adawa ta NNPP a jihar Kano ta ce, ta bankaɗo wani shiri da jam’iyyar APC mai mulki ke yi na rage yawan mutanen da ke da katin yin zaɓe a jihar ta hanyar siye su a wajen masu su.

Jaridar Solacebase ta ruwaito cewa, hakan na faruwa ne dai-dai lokacin da jam’iyyar ta NNPP ke cewa yanzu haka a karon farko a tarihin mulki a jihar Kano, masu rike da madafun ikon Gwamnati ke mayar da al’amuran gwamnati tamkar na iyali musamman la’akari da nade-naden mukamai.

Sanarwar ta ce hakan na nuni da yadda gwamnatin jihar ta yi watsi da babban nauyin da ya rataya a wuyanta na kare rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa ta hanyar tada hankali, nuna son rai, da kuma wadatar da kai da yan uwa.

A cewar sanarwar hadin gwiwa da shugaban taron, Garba Diso da sakataren kungiyar Dokta Hamisu Sadi Ali suka sanyawa hannu a kokarin neman mafita cikin gaggawa kan barazanar da ake fuskanta, kwamitin ya yi kira ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa da ta buga tare da liƙa sunayen duk masu katin zaben da ba a karba ba domin a wayar da kan masu haƙƙin mallakar su.

‘’Daga cikin sauran batutuwan da taron bitar ya fitar, ya yi nuni dacewa an samu rugujewar tsarin ilimi biyo bayan Rufe makarantun hadin kai da na kwana; rashin biyan kudin jarrabawar da gwamnatin jihar ta yi wa WAEC, NECO, da NBAIS; jinkiri da rashin biyan alawus na tallafin karatu ga daliban kasashen waje da na gida; da kuma samar da yanayi na rashin ilimi a cikin harabar makarantu ta hanyar gina shagunan kwana a makarantu kamar Jami’ar Arewa maso Yamma Kano,” in ji sanarwar.

‘’Saboda haka taron na nuna matukar damuwarsa kan ambaliyar ruwa da rugujewar gine-ginen da suka auku kwanan nan a kasuwannin Kantin Kwari da na Civic Centre wanda ya yi sanadin asarar rayuka da dukiyoyi da sauransu.

Haka kuma taron bitar ya bayyana goyon bayan jam’iyyar NNPP kacokan a jihar, inda ya jaddada cewa lallai zaben 2023 ya bambanta da wanda ya gabata, ya zama dole jam’iyyar ta yi duk abin da ya dace cikin tanadin doka don ganin zaben 2023 ya sami ‘yanci da adalci.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet