Labarai
Ba Dan Gwamnatin Buhari Ba Da Najeriya Ta Durkushe
Mataimakin daraktan dabarun sadarwa na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa a jam’iyyar APC, Lanre Issa-Onilu, ya ce ‘yan Najeriya na hakuri saboda sun amince da gwamnatin da APC ke jagoranta.
Ya kuma ce amma ba dan shugabancin shugaban kasa Muhammadu Buhari ba, da Najeriya ta durkushe.
“Zan iya gaya muku idan ba don Buhari ba, wata kila kasar nan ta fadi, a lokacin mulkin PDP sojojinmu suna ta yawo a kan iyaka saboda ba su da makaman yaki,” in ji Issa-Onilu a wata hira da gidan talabijin na Channels TV a shirin Sunrise Daily.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, Ya kara da cewa, “Hakuri ya zo da amana, akwai wani matakin amincewa da ‘yan Najeriya suka yi da APC sama da shekaru bakwai, wannan gwamnati ta iya nuna wasu alkawuran da ta (yi) ‘yan Najeriya suka ce za mu iya amincewa da ku.
“Yan Najeriya ba wawaye ba ne. Idan babu amana, kamar yadda ya faru a karkashin PDP da suka ba da lokaci mai tsawo. Bayan shekaru goma ne ‘yan Najeriya suka fara mayar da martani lokacin da suka rasa imani gaba daya,” in ji shi.
