Connect with us

Labarai

Wani Manomi Ya Rasa Ransa, Yayin Da Mutane 8 Suka Tsallake Rijiya Da Baya

 

Wani iftila’i da ya afku a ranar Lahadi a unguwar Kabala Doki da ke karamar hukumar Kaduna ta Arewa, yayin da wani manomi ya nutse a ruwa tare da wasu mutum takwas da suka tsira daga hatsarin kwale-kwale a jihar.

Daily Trust ta tattaro cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 8:30 na safiyar ranar Lahadi inda wanda abin ya shafa, mai suna Umar, ya taka kwale-kwalen domin taimakawa mutanen da suka makale a gefen kogin amma kwale-kwalen ya kife.

Wani mazaunin garin da ya bayyana sunansa da Murtala Kabala ya shaida wa Daily Trust cewa wanda ya mutum ya shahara a tsakanin al’umma kuma yana da wata gona da ke kusa da kogin.

“Abin damuwa ne saboda Umar ya san yin iyo kuma ya kasance a bakin kogi tsawon shekaru yana noma. Wannan ne ya sa muka yi mamakin samun labarin cewa ya nutse a cikin kogi daya a lokacin da yake kokarin ceto mutanen da suka makale a wancan gefen kogin. Allah ya gafarta masa kurakuransa,” inji shi.

An fahimci cewa Umar ne kawai ya nutse; sauran da ke cikin jirgin sun tsira.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Shugaban karamar hukumar Kaduna ta Arewa, Muktar Baloni, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya shaida wa Daily Trust cewa har yanzu ba a gano gawarsa ba.

Ya koka da yadda wani bangare na karamar hukumar ya samu ambaliya, yana mai cewa Ƙaramar Hukumar tana cigaba da tattara bayanai na gidajen da abin ya shafa domin taimakawa wadanda abin ya shafa.kuma ka

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet