Labarai
Gwamnatin Kano Ta Daga Darajar Asibitin Rano Zuwa Asibitin Kwararru
Gwamnatin jihar Kano ta daga dajarar asibitin garin Rano zuwa asibitin kwararru mai dauke da gadaje dari hudu.
Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje shine ya sanar da hakan a yammacin ranar Talata, yayin da yake jawabi a wurin taron bikin kaddamar da asibitin da aka gudanar a harabar sa da ke garin Rano.
Yace gwamnatin kano tun bayan samar da masarautu biyar da tayi ta dauki aniyar samar da asibitocin kwararru a daukacin masarautun jihar nan da nufin saukakawa mazauna garuruwa da kyaukan jihar kano hanyar samun kulawar jami’an lafiya yadda ya kamata kuma akan lokaci.
Da yake jawabi Sarkin Rano Alhaji Kabiru Inuwa ya godewa gwamnatin kano bisa kokarin inganta harkokin kiwon lafiya a masarautar.
Sarkin na Rano ya kuma yi kira ga al’umar masarautar da suyi kyakykyawan amfani da damar da suka samu ta wannan asibiti da a cewar sa tazo dai dai lokacin da mazauna yankin ke bukatar karuwar kwararrun jami’an kiwon lafiya don rage kalubalen da suke fuskanta.
