Uncategorized
Rashin biyan Garatuti: Ƴan Fansho sun yi zanga-zangar lumana
Rashin biyan ƙuɗaɗen Garatuti, ya sanya wasu ƴan Fansho gudanar da zanga-zangar lumana a jihar Neja.
A Larabar makon nan ne da dama daga cikin ƴan fanshon suka mamaye gidan gwamnatin jihar da ke birnin Minna, domin nuna rashin jin dadin su na rashin biyansu kudaden nasu har na tsawon shekaru takwas.
A zantawarsa da manema labarai guda cikin masu zanga-zangar Malam Idris Ndalati, wanda ya yi ritaya a matsayin babban direba a gidan gwamnati, ya shaida cewa shekaru bakwai kenan ba a biya shi kuɗin garatutinsa ba.
A cewarsa, da dama daga cikin wadanda suka yi ritaya a jihar Nijar sun mutu, yayin da wasu kuma suka kamu da cutukan hawan jini da kuma yajin aiki sakamakon matsalolin da ke da nasaba da rashin biyansu hakkokinsu.
Haka kuma ya ce, “ƴaƴanmu sun daina zuwa makaranta saboda ba za mu iya biyan kudin makaranta ba, kuma da yawa daga cikinmu ba za su iya sauke nauyin ciyar da iyalinmu ba.”
Masu zanga-zangar sun kuma zargi kungiyar ‘yan fansho ta Najeriya reshen Nijar da rashin kare muradun mambobinta dasuka kammala aiki.
Da yake jawabi ga masu zanga-zangar, mataimakin gwamnan jihar Alhaji Ahmed Ketso, ya ce gwamnatin jihar za ta duba ƙorafin da suka gabatar.
