Jaridar Solacebase ta ruwaito cewa, Mai magana da yawun hukumar na ƙasa Mista Femi Babafemi, ne ya bayyana hakan.
Femi ya ce, jami’an hukumar sun kama mutumin ne a unguwar Sate, Mararraban Tola da ke yankin ƙaramar hukumar Mayo Belwa ta jihar Adamawa.
Haka kuma ya ƙara da cewa an kama shi ne a gonarsa da yake noman tabar.
