Connect with us

Ilimi

Gwamnatin Tarayya Ta Bada Umarnin A Bude Makarantun Jami’o’i

Gwamnatin tarayya a ranar Litinin din nan ta umurci shugabannin jami’o’i da su sake bude makarantu tare da baiwa dalibai damar komawa karatu, nan take.

Ku tuna cewa Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) ta kwashe kimanin watanni bakwai tana yajin aikin saboda kungiyar na neman Gwamnatin Tarayya ta ba da tallafin farfado da Jami’o’in Gwamnati da kudaden alawus-alawus na Jami’o’i da basussukan karin girma.

Sauran sun hada da sake tattaunawa kan yarjejeniyar ASUU-FG ta 2009 da kuma rashin daidaito a Tsarin Bayanan Biyan Albashin Ma’aikata.

To sai dai kuma duk da takun sakar tsakanin kungiyar ta ASUU da Gwamnati, gwamnatin tarayya ta garzaya kotu domin kalubalantar matakin da kungiyar ta dauka.

A makon da ya gabata ne babbar kotun da’ar ma’aikata ta kasa ta hannun Polycarp Hamman, alkali a hukumar NIC, ta amince da bukatar gwamnatin tarayya na neman shiga tsakani domin hana ASUU ci gaba da yajin aikin.

Tuni dai ASUU ta shigar da daukaka kararraki 14 na domin kalubalantar umarnin.

Sai dai kuma gwamnatin tarayya ta gaji da yajin aikin, inda hukumar kula da jami’o’i ta kasa ta umurci shugabannin jami’o’in da su sake bude makarantu tare da barin dalibai su koma karatu.

Gwamnatin tarayya a cikin wata wasika da ta bayyanawa manema labarai a ranar Litinin din nan, mai dauke da sa hannun daraktan kudi da asusun NUC, Sam Onazi, a madadin babban sakataren hukumar, Farfesa Abubakar Rasheed, ta umurci dukka shugabannin; jaglrori da shugabannin majalissar gudanarwa na jami’o’in tarayya da su sake bude makarantu.

Wasikar tana cewa: “Tabbatar da cewa ‘yan kungiyar ASUU nan da nan su koma tare da fara karatu; Dawo da ayyukan yau da kullun na makarantun Jami’o’i daban-daban.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetDeneme Bonusu Veren SitelerCasibomcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahisjojobetjojobetjojobetjojobet girişmarsbahisjojobetgrandpashabetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet girişjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobetjojobetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet