Labarai
TCN Ya Sanar Da Dawowar Wutar Lantarki a Fadin Kasar Nan
Kamfanin dakon wutar lantarki na Kasa (TCN) ya ce an maido da layin wutar a kasar da ya dauke a safiyar ranar Litinin din nan.
“An fara dawo da sashin layin da abin ya shafa kai tsaye da karfe 11.55 na safe inda Osogbo da Ihovbor suka koma grid sai Jebba da Osogbo, Kainji da Jebba, Benin da Onisha, Shiroro da Kaduna, Shiroro da Katampe, da Alaoji da Ikot. Ekpene, ”in ji shi a cikin wata sanarwa a ranar Litinin.
“Sauran sun hada da Lokoja da Gwagwalada, Odukpani da Ikot Ekpene, Benin da Omotosho, Oke-Aro da Ikeja west, Egbin da Oke-Aro and Kaduna da Kano.”
