Labarai
Da ɗumi-ɗumi: Allah ya yi wa Yakubu ka fi Gwamna rasuwa
Allah ya yi wa Alhaji Umar Malumfashi wanda aka fi sani da Bankaura da kuma Yakubu ka fi Gwamna a cikin shirin Kwana Casa’in rasuwa.
Marigayin dai tsohon jarumi ne a masanatar shirya Fina-finai ta Kannywood.
Za mu kawo ci gaban labarin rasuwar tasa a nan gaba.
Muna roƙon Allah ya gafarta masa kurakurensa, ya kuma sa aljanna ta zama makoma a gareshi.
Idan tamu tazo Allah yasa mu cika da imani.
