Siyasa
Rashin girmama dattawa jam’iyya: APC ta dakatar da ɗan Majalisar jiha
Jam’iyyar APC mai mulki a jihar Jigawa, ta dakatar da ɗan majalisar dokokin jihar mai wakiltar mazaɓar Kanya Babba watau Honarabul Usman Haladu Isah, sakamakon zarginsa da yiwa jam’iyyar zagon ƙasa a shirye-shiryenta na lashe zaɓen baɗi.
Hakan na ƙunshe ne ta cikin wata sanarwar da jam’iyyar ta raba wa manema labarai wadda shugaban jam’iyyar na ƙaramar hukumar Babura Isa Ubale da shugaban jam’iyyar a yankin Kanya Babba suka sanya wa hannu.
Sanarwar ta ce ana zargin ɗan majalisar da yiwa jam’iyyar zagon ƙasa da kuma rashin mutunta dattawan jam’iyyar.
Sanarwar ta kuma ruwaito cewa, dakatarwar ta fara aiki ne daga ranar 24 ga watan Satumban bana har sai an kammala bincike don ci gaba da daukar mataki.
Ta cikin sanarwar dai, Ubale ya ce, dukkan jiga-jigan jam’iyyar na mazaɓar sun amince da dakatarwar.
Haka kuma sun ce, Dakatarwar ta fara aiki ne tun daga ranar 24 ga wannan watan da muke ciki na Satumba har zuwa lokacin da aka kammala bincike a kan dakataccen mamban na APC.
A baya-bayan nan ne ɗan majalisar ya rasa tikitin tsayawa takara a hannun abokin karawarsa Ibrahim Hashim Kanya a zaben fidda gwani na jam’iyyar ta APC a zaɓen baɗi.
