Wasu ƴan bindiga da ake kyautata zaton ƴan fashin daji ne, sun hallaka basarake a garin Mohoro tare da wasu mutane goma sha biyu.
Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne bisa ƙin amincewar basaraken kan al’ummar yankinsa su biya harajin da ƴan bindigar suka ɗora wa mutanen yankin.
Wannan abun tashin hankali ya faru ne a yankin ƙaramar hukumar Mariga mai Iyaka da Jihohin Zamfara da Kebbi a karshen makon da muka yi bankwana da shi.
Tuni dai gwamnatin Jihar ta Neja ta yi Alla-wadai bisa aikata ɗanyen aikin, inda Sakataren gwamnatin Jihar Alhaji Ahmed Ibrahim Matane ya ce sun tura ƙarin jami’an tsaro yankin, kuma hankali ya kwanta a warin.
Jaridar Solacebase ta ruwaito cewa, Ita ma rundunar ‘yan sanda ta Jihar Neja ta tabbatar da aukuwar lamarin, kuma kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Monday Bala Kuryas ya ce suna daukar mataki.