Labarai
Babban Sufetan Yan Sanda Ya Sha Alwashin Gudanar Da Zaben 2023 Cikin Kwanciyar Hankali
Babban Sufeto Janar na ‘yan sandan Kasae nan, IGP Usman Alkali, ya bayar da tabbacin cewa rundunar ‘yan sandan za ta hada gwiwa da ‘yan uwa jami’an tsaro domin ganin an gudanar da zaben 2023 cikin kwanciyar hankali.
Alkali, wanda DCP Basil Idegwu, shugaban rundunar ‘yan sandan tarayya ya wakilta, ya bayyana haka a wata tattaunawa kan manufofin tsaro mai taken “2022 General Election wato Babban Zaben 2022: rashin tsaro a matsayin barazana ga kundin tsarin mulki”, wanda Cleen Foundation tare da hadin gwiwar Ford Foundation suka shirya a ranar Larabar nan a Abuja.
Ya ce rundunar ‘yan sandan na kokarin ganin ta ci gaba da samun ci gaba wajen gudanar da ayyukan jami’an tsaro a zaben Osun, Ekiti da Anambra, gabanin babban zaben 2023.
“Mun samu babban yabo daga masu sa ido na kasa da kasa da masu sa ido na cikin gida kan yadda hukumomin tsaro suka suka taka a zaben Ekiti da Osun.
“Wannan ya nuna shirye-shiryen rundunar ‘yan sandan Najeriya da sauran jami’an tsaro don tabbatar da sahihin zabe ya wakana a 2023.
“’Yan sanda suna tuntubar duk masu ruwa da tsaki a harkar tsaro don raba bayanan sirri masu inganci, aiwatar da hadin gwiwa da tsare-tsare daban-daban da aiwatar da ayyuka wadanda ke samun riba a halin yanzu.
“Duk da haka, ya zama wajibi a lura cewa a al’amuran tsaro, kowane dan kasa mai ruwa da tsaki ne, shi ya sa ake yaba wa wannan shiri da aka shirya domin tattaunawa.
“Saboda dole ne kowa da kowa ya tashi tsaye don ganin an yaki matsalar rashin tsaro a kasar nan,” in ji shi.
Baba ya ce ta hanyar yin amfani da nasarorin da aka samu a zabukan Edo, Ondo da Anambra, ‘yan sanda za su tabbatar da gudanar da zaben 2023 cikin kwanciyar hankali.
Ya ce, ta hanyar karfafa matakan tsaro, ‘yan sanda sun tsara shirye-shiryen horar da jami’ansu a fadin kasar nan.
Ya ce shirye-shiryen horarwar sun hada da horarwa kan harkokin tsaro da sauran su, don tabbatar da cewa ‘yan kasa sun yi amfani da ikonsu ba tare da tsoron cin zarafi ko tsoratar da masu aikata laifuka a zaben 2023 ba.
