Labarai
Gwamnatin tarayya ta sanar da ranar 3 ga Oktoba a matsayin ranar hutu
Gwamnatin tarayya ta sanar da ranar Litinin ɗin makon gobe watau 3 ga watan Oktoba a matsayin ranar hutun bikin cikar Najeriya shekaru 62 da samun ƴancin kai.
Ministan harkokin cikin gida Alhaji Ra’uf Aregbesola ne ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar ta hannun babban sakataren ma’aikatarsa Dakta Shuaib Belgore.
Ta cikin sanarwar dai, Ministan ya taya ‘yan Najeriya murnar bikin tare da ba da tabbacin aniyar gwamnati na tinkarar kalubalen da al’ummar kasar ke fuskanta da kuma sanya walwala a zukatan al’ummar Najeriya.
Sanarwar ta ce, “Duniya na fama da matsalolin tattalin arziki da tsaro wadanda kuma suka shafi al’ummarmu”.
Haka kuma Aregbesola, ya nanata ƙudirin gwamnatin tarayya na haɗa kan ƙasashe da kuma ganin kasa Najeriya ta samu ci gaba.
Ya kuma hori ƴan Najeriya da su yi amfani da wannan lokaci wajen yin tunani kan ƙalubalen da al’ummar ƙasar ke fuskanta da kuma rawar da za su iya takawa wajen magance su.
