Connect with us

Labarai

Dalilin Da Yasa Tinubu Ya Tafi Landan Bai harci Sanya Hannun Yarjejeniyar Zaman Lafiya Ba

 

 

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, ya tafi Landan ne domin ya huta, kamar yadda mamba a kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC, Ayo Oyalowo, ya bayyana.

Rashin halartar Tinubu a wajen taron yarjejeniyar zaman lafiyar da aka yi a ranar Alhamis din nan ya janyo ce-ce-ku-ce, inda aka rika yada jita-jitar cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyya mai mulki ba shi da lafiya.

Amma da yake magana a wani shirin gidan talabijin na ARISE TV, Oyalowo ya ce, “Asiwaju Bola Ahmed Tinubu yana Landan. Ba zai iya hutawa a Legas ba, ba za su bar shi ya huta ba. Yawancin lokaci yakan zo Abuja, kuma yanzu ba za su bar shi ya huta ba. Wannan mutumin yana aiki na tsawon sa’o’i 20 a cikin sa’o’i 24 a kowace rana. Don haka masu hankali sun ga ya kamata ya bar kasar domin mutane ba za su bar shi ya huta ba tunda yakin neman zabe na nan tafe.

“Gayyatar yarjejeniyar zaman lafiya ta zo ne bayan da Tinubu ya bar kasar. Ko da abokin takararsa Sanata Kashim Shettima ba ya gari, dole ya bar abin da yake yi a Maiduguri.”

Ba kamar Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP ba, wanda ya bayyana tafiyarsa zuwa Dubai a satin da ya rage kafin yakin neman zaben, tawagar Tinubu da a baya ta bayyana tafiyar tasa, ta yi shiru a wannan karon.

Lokaci na ƙarshe da rashin halartar Tinubu a taron jama’a ya jawo cece-kuce shi ne a taron shekara-shekara na kungiyar lauyoyin Najeriya (NBA) da ya gidana a Legas.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleripadişahbettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xgrandpashabetgrandpashabetpusulabetvdcasinograndpashabetgrandpashabet girişgrandpashabetholiganbetmarsbahismarsbahismarsbahisjojobetjojobetholiganbetholiganbetjojobetjojobet girişjojobet güncel girişjojobet güncel girişcasibompusulabetpusulabetcasibom girişcasinolevantcasinolevantmatbetholiganbetholiganbet girişcasibomcasibom girişjojobetjojobet girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabetcasibomcasinolevantgrandpashabetcasibomsekabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet