Connect with us

Labarai

Gwamnatin tarayya ta gargaɗi ƙungiyar ASUU bisa rashin martaba umarnin kotu

Gwamnatin tarayya, ta gargaɗi ƙungiyar malaman jami’o’i ASUU bisa ƙin karɓar  umarnin kotun Ma’aikata da ta basu na janye yajin aiki.

Ministan ƙwadago da Nagartar Aiki Dakta Chris Ngige ne ya yi jan kunnen ta cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun mataimakin daraktan yaɗa labarai da hulda da jama’a na ma’aikatar Olajide Oshundun a jiya Lahadi.

Haka kuma ta cikin sanarwar, ministan ya shawarci malaman da ke yajin aikin da su daina daukar doka a hannunsu ta hanyar umurtar mambobinta da su ci gaba da yajin aikin na watanni takwas.

Chris Ngige ya kuma ce, Yajin aikin ƙungiyar ya saba wa umarnin shiga tsakanin da hukumar ta NICN wanda ya hana kungiyar daukar kowane irin mataki.

Ya zargi shugabannin ƙungiyar da yin gaban kansu tare da yaudarar mambobinsu.

Ministan ya kuma jaddada kira ga ƙungiyar da ta mutunta umarnin kotu tare da komawa bakin aiki yayin da ake tattaunawa kan sauran batutuwan da ake taƙaddama a kan su.

Haka kuma, Sanarwar ta musanta rahotannin da ke cewa ministan fice a fusace ana tsaka yin taro tsakanin majalisar wakilai da kungiyar ASUU ta gudanar a ranar 29 ga watan jiya na Satumba.

Sanarwar ta ce ministan ya bar gurin taron ne domin halartar wasu muhimman batutuwa bisa ga izinin shugaban majalisar wakilai Femi Gbajabiamila bayan ya gabatar da jawabinsa.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet