Labarai
Taraba: Ƴan bindiga sun hallaka mutane 12
Rahotonni daga Ƙaramar hukumar Bali da ke Jihar Taraba na nuni da cewa, Wasu ƴan bindiga da ba a kai ga gano su ba sun hallaka mutane goma sha biyu.
BBC ta ruwaito cewa iftila’in ya faru ne a ƙauyen Mubizen jiya Lahadi.
Haka kuma ta ce, shugaban ƙungiyar makiyaya na Jihar ta Taraba Ardo Umar Bello, ya tabbatar mata da cewa ƴan bindigar sun je garin ne sanye da kakin jami’an sintiri na Vigilante.
Ya ƙara da cewa ɓata garin sun tara mutane ne a wani waje inda suka shaida musu cewa sun je domin su kama wasu masu laifi ne amma sai kawai suka bude musu wuta tare da kashe mutanen goma sha biyu.
Ardo Umar Bello, ya ƙara da cewa mutane hamsin sun ɓata yayin guje wa harbe-harben ƴan bindigar.
Haka kuma ya ce, cikin waɗanda suka ɓatan har da mata da ƙananan yara.
BBC ta kuma ruwaito cewa ƴan bindigar sun arce da shanu guda ɗari da talatin.
Ta kuma bayyana cewa jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar ASP Usman Abdulahi, ya tabbatar da aukuwar lamarin, sai dai ya ƙara da cewa sun kama mutum huɗu daga cikin ƴan bindigar.
