Labarai
Dan Takarar Shugaban Kasa Na APC Zai Dawo Najeriya Nan Ba Da Jimawa Ba – Keyamo
Festus Keyamo ya ce nan ba da jimawa ba dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Bola Tinubu zai dawo kasar nan.
Kakakin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC (PCC) ne ya bayyana hakan a ranar Larabar nan biyo bayan nuna damuwa kan ci gaba da zaman Tinubu a Birtaniya.
“Na san zai dawo nan da kwanaki biyu. Ina da wannan bayanin. Ban san takamaiman ranar ba, ”in ji Ministan kwadago da tabbatar da nagartar aiki ga Gidan Talabijin na Channels a ranar Larabar nan. “Ba zan iya cewa Juma’a ko Asabar ba amma na san zai dawo nan ba wasu kwanaki.”
Ziyarar da Tinubu ya kai kasar Birtaniya ta dauki hankula a ‘yan kwanakin nan. Masu suka sun yi iƙirarin rashinsa lokacin da aka fara yaƙin neman zaɓe na siyasa yana nuna cewa za a iya samun matsala. Wasu kuma na ikirarin cewa tsohon gwamnan jihar Legas yana ziyarar jinya ne a kasar Birtaniya.
Dangane da cece-kucen kan rashin sa a kasar ya janyo, Tinubu ya fitar da wani faifan bidiyo na motsa jiki na tsawon dakika bakwai, yana mai cewa ya cancanta ya jagoranci kasar sabanin zarge-zargen.
Kuma da aka tambaye shi ko mai rike da tutar jam’iyyar APC yana Landan ne a wata ziyarar jinya, Keyamo ya ce, “Ba ni da irin wannan bayanin”, yana mai cewa “Ina magana ne ga kwamitin yakin neman zabe ba na dan takara ba”.
