Featured
Gasar cin kofin Duniya ta bana za ta zamo karshe gareni- Messi
Daga Abdu Ado Ƙofar Na’isa
Dan wasan gaba na PSG Lionel Messi ya ce tabbas gasar cin kofin duniya da za ta gudana a Qatar cikin watan Nuwamba mai zuwa za ta zamo ta karshe gareshi da za a ga haskawarsa a fili.
Dan wasan na Paris St-Germain mai shekaru 35 ya dokawa kasarsa Argentina makamanciyar gasar ta cin kofin duniya har 4 a tarihi, kuma ya ci kwallaye 6 sannan ya taimaka aka ci 4 a wasanni 19 da ya doka.
A shekarar 2014 ne, Messi ya yi nasarar kai Argentina matsayin ta 2 a gasar ta cin kofin duniya da ta gudana a Brazil, yayinda kuma ya jagoranci kasarsa a matsayin kyaftin zuwa gasar nahiyar kudancin Amurka ta Copa America wanda suka lashe kofin, wanda ke nuna cewa zuwa yanzu kofin da ba shi da shi kawai shi ne kofin duniya.
A ganawarsa da wata kafar yada labarai a Turai, Messi ya bada tabbacin cewa gasar kofin duniya mai zuwa ce gasar karshe da za a yi da shi a matsayin dan wasa.
A shekarar 2005 ne Messi ya fara buga wa babbar tawagar kasar sa wasa, inda daga nan ya buga wasanni 164, ya kuma ci kwallaye 90.
