Connect with us

Ilimi

Kotun Daukaka Kara Ta Umarci Kungiyar ASUU Ta Koma Aiki Ba Tare Da Bata Lokaci Ba

Kotun daukaka kara da ke Abuja, ta umarci mambobin kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) da su koma bakin aiki ba tare da bata lokaci ba.

Kotun daukaka kara ta bayar da wannan umarni ne a wani hukunci da ta yanke kan bukatar da kungiyar ta ASUU ta yi na neman a ba ta izinin daukaka kara kan umarnin babbar kotun da’ar ma’aikata ta kasa wadda ta bukaci malaman da ke yajin aiki su koma bakin aiki.

Kotun ta kuma bayar da izinin daukaka kara kan umarnin kotun masana’antu, tare da jaddada cewa ASUU ta bi umurnin karamar kotu daga yau 7 ga watan Oktoba.

Kwamitin mutum 3 da mai shari’a Hamman Barka ya jagoranta, ya ce ASUU ta gabatar da sanarwar daukaka kara a cikin kwanaki 7, dole ne ta nuna shaidar cewa mambobinta sun koma bakin aiki nan take.

Kwamitin ya ce rashin bin umarnin, zai sa karar ta gaza karbuwa a gaban kotun daukaka karar.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet